Kawu Sumaila Ya Tallafa Wa Masu Amfani da Kafafen Sada Zumunta a Kano ta Kudu

0
7

Sanata Kawu Sumaila, mai wakiltar Kano ta Kudu, ya raba tallafin kudi na Naira dubu ɗari biyar-biyar ga matasa 16 da suka shahara wajen amfani da kafafen sada zumunta a mazabar sa.

Wannan mataki na daga cikin sanatan na ci gaba da tallafa wa matasa da bunkasa harkokin kasuwanci, tare da amfani da damar da ke cikin kafafen sada zumunta wajen haɓaka cigaban a’lumma.

Sanata Kawu ya bayyana cewa, wannan shiri zai taimaka wajen mayar da amfani da kafafen sada zumunta daga dandalin tattaunawa zuwa ingantattun ayyukan dogaro da kai da za su haifar da tasiri mai kyau a rayuwar yau da kullum.

Waɗanda suka ci gajiyar tallafin sun nuna farin ciki da godiya, tare da alƙawarin amfani da kuɗin wajen ƙirƙirar ayyuka masu ma’ana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here