Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin samar da kulawar lafiya kyauta ga dukkan fursunoni a gidajen gyara hali na jihar, karkashin hukumar taimakekeniyar lafiya ta KSCHMA.
Shugabar hukumar, Dr. Rahila Mukhtar, ta bayyana cewa an kafa tawaga ta musamman da za ta rika ba wa fursunoni kulawar lafiya yadda ya dace, domin tabbatar da ingantacciyar rayuwa yayin da suke tsare.
A nasa jawabin, shugaban hukumar gidajen gyara hali na ƙasa a Kano, Sylvester Nwakuche, ya jinjinawa gwamnatin jihar bisa wannan mataki, yana mai cewa hakan babban taimako ne ga hukumar da kuma fursunonin.