Al’ummar Kurfi sun yi sulhu da ƴan bindiga a Katsina

0
10

Shugabannin al’umma a ƙaramar hukumar Kurfi, Jihar Katsina, sun jagoranci zaman sulhu da wasu jagororin ƴan bindiga domin kawo ƙarshen matsalolin tsaro da suka addabi yankin.

A ranar Alhamis aka rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiyar a dajin Wurma, karkashin jagorancin Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi, da shugaban ƙaramar hukumar, Babangida Abdullahi Kurfi.

Daga cikin jagororin ƴan bindigar da suka shiga yarjejeniyar akwai Alhaji Usman Kachalla Ruga, Sani Muhindinge, Yahaya Sani (Hayyu) da Alhaji Shu’aibu.

Ƴan bindigar sun amince da ajiye makamai tare da sakin mutanen da suke tsare da su, kana suka yi alƙawarin ba za su hana manoma komawa gona ba.

Kurfi ta shiga jerin ƙananan hukumomi na Katsina da suka shiga irin wannan yarjejeniya da ƴan bindiga, bayan Jibia, Batsari, Safana da Dan musa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here