Rundunar Hisbah ta Karamar Hukumar Garun-Malam, Jihar Kano, ta bayyana cewa ta samu nasarar fasa giya sama da kwalabe 200 a cikin shekarar da ta gabata.
Babban Kwamandan rundunar, Ustaz Muhammad Nasir Rabiu, ya ce jami’an Hisbah sun gudanar da samame da bincike a wurare daban-daban, inda suka kama giyar da aka lalata nan take.
Ya ce hukumar ta baza jami’ai a fadin karamar hukumar domin dakile shigo da giya da sauran kayayyaki masu sabawa koyarwar addini da dokar Jihar Kano.
Ustaz Nasir ya kuma jaddada cewa siyar da giya ko shan ta babban laifi ne a Kano, don haka rundunar za ta ci gaba da sa ido don hana bata-gari aikata hakan.
Kwamandan ya bayyana cewa kasuwar Kwanar Gafan, wadda aka rufe tun bayan kammala kasuwar tumatur, na cikin wuraren da ake sanya ido sosai domin tabbatar da bin doka da oda a yankin.