Ni da Makinde zamu yi kokari idan PDP ta tsayar damu takarar shugaban ƙasa–Gwamnan Bauchi

0
8

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce shi da gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, za su yi kyau a tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2027. 

Ya bayyana haka ne a wata hira da talabijin ta Channels, inda ya ce PDP na bukatar Kirista daga Kudu a matsayin shugaban kasa tare da Musulmi daga Arewa a matsayin mataimaki. 

Bala ya ce hakan zai taimaka wajen mutunta bambancin addini da kabilu a Najeriya, tare da guje wa kuskuren da APC ta yi a 2023 da batun tikitin Musulm-Musulm. 

Ya ƙara da cewa PDP ba ta riga ta zaɓi wani mutum da zai yi mata takarar shugaban ƙasa ba, amma tana da buƙatar yin taka-tsantsan wajen tsayar da dan takara domin samun nasara a 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here