Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa al’ummar jihar na ci gaba da gode wa Allah duk da kalubalen da suka fuskanta a tsawon shekaru.
A tattaunawa da yayi da BBC, shekara guda bayan mummunar ambaliyar ruwan da ta tilastawa dubban mutane barin gidajensu a Maiduguri sakamakon fashewar madatsar ruwa ta Alau, Zulum ya ce gwamnatin jihar ta dauki matakan kariya don kauce wa sake faruwar irin wannan bala’i a bana.
Ya bayyana cewa aikin faɗaɗawa da yashe madatsar ruwan Alau na daga cikin muhimman matakan da gwamnati ta aiwatar, musamman ganin cewa hukumar yanayi ta kasa (NIMET) ta yi gargadin yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu jihohi ciki har da Borno a daminar 2025.
Borno ta daɗe tana fama da rikicin Boko Haram wanda ya ɗauki kusan shekaru 15, lamarin da ya yi sanadin asarar dubban rayuka tare da tilasta miliyoyin jama’a barin muhallansu.