Gamayyar kungiyoyin cigaban yankin Bakin Kasuwar kurmi dake ƙwaryar birnin Kano, sun mika sakon godiya ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa amincewar sa da sanya fitilun titi a yankin, musamman a Zawiyyar Sheikh Tijjani Usman Zangon Bare Bari.
A cewar kungiyoyin, wannan aiki ya zo a lokaci mai muhimmanci, ganin cewa ana shirin gudanar da babban taron Mauludin Annabi (SAW) a zawiyyar, wanda fitilun za su taimaka wajen samar da haske da kuma inganta tsaro yayin taron.
Sun ce amincewar Gwamnan cikin gaggawa da kulawa ta nuna yadda gwamnatin sa ke bai wa bukatun al’umma muhimmanci.