EFCC Ta Kama Dan’uwan Shugaban NAHCON Kan Zargin Badakalar Biliyan 50

0
9

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta kama Sirajo Salisu Usman, dan’uwan shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), bisa zargin sa da hannu a badakalar Naira biliyan 50 da ta shafi shirye-shiryen aikin Hajjin bana.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an cafke Sirajo, wanda shi ma darakta ne a ofishin shugaban hukumar, a ranar Laraba a Abuja, kuma yana ci gaba da kasancewa a hannun EFCC.

Rahotanni sun ce binciken ya shafi almundahanar kudaden da suka shafi Naira biliyan 25 da aka kashe kan tanti a Masha’ir, Naira biliyan 1.6 na alawus ga iyalan jami’ai, da kuma Naira biliyan 8 da aka ware don masauki na gaggawa a birnin Makkah.

Wasu ma’aikata sun bayyana cewa Sirajo ya kasance tamkar “shugaba na ainihi” wanda ke da hannu wajen amincewa da kwangiloli da kuma tafiyar da kudade a hukumar.

Sai dai hukumar ba ta fitar da sanarwa kai tsaye ba kan kama shi. Kakakin NAHCON, Fatima Usara, ta ce “al’ada ce ta bincike,” duk da cewa majiyoyi sun tabbatar cewa binciken ya shafi zargin karkatar da kudi, cin hanci da kuma amfani da ofis ba bisa ka’ida ba.

Hukumar NAHCON dai na fuskantar matsin lamba daga masu ruwa da tsaki da ke kira da a gudanar da cikakken bincike da kuma tsige shugaban ta, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, wanda aka fi sani da Pakistan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here