Ba zamu bari ASUU ta shiga yajin aiki ba—Gwamnatin tarayya

0
5

Ministan Ilimi, Maruf Tunji Alausa, ya tabbatar wa ɗalibai cewa zanga-zangar da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta yi a baya-bayan nan ba za ta rikide zuwa yajin aiki ba.

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, jim kaɗan bayan wani muhimmin taro da jami’an gwamnati domin tattaunawa a kan bukatun ASUU.

Alausa ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kuduri aniyar kawo ƙarshen rikicin da ya daɗe yana janyo tsaiko a jami’o’i, tare da tabbatar da cewa ba za ta sake sanya hannu kan yarjejeniyar da za ta zama mai wuyar aiwatarwa ba.

“Shugaba Tinubu ya umurci ma’aikatar ilimi da sauran hukumomin gwamnati da su haɗa kai wajen samar da mafita ta dindindin wacce za ta yi daidai da tsarin doka da kuma tattalin arzikin ƙasa,” in ji shi.

Ministan ya kuma shaida cewa bashin kuɗaɗen albashin malaman jami’a da ya kai kashi 35 cikin ɗari za a biya shi nan gaba, bayan an fara biyan sauran ma’aikatan gwamnati.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here