Wata kotu a Kano ta bayar da umarni ga mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan sanda na Shiyya ta ɗaya da ya gudanar da cikakken bincike kan zargin laifin ɓata suna da ake yi wa mawallafin jaridar Daily Nigerian, Jafar Jafar.
Wannan na zuwa ne bayan ƙarar da Daraktan tsare tsare na Fadar Gwamnatin Kano, Hon. Abdullahi Ibrahim Rogo, ya shigar a gaban Babbar Kotun Majistire ta No. 15 da ke ƙarƙashin jagorancin Malam Abdul’aziz M. Habib.
Rogo ya kai ƙarar Jafar Jafar tare da Audu Umar, bisa zargin sun wallafa labaran ƙarya a shafin Daily Nigerian da suka zubar masa da mutunci da kuma mutuncin gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.
A cewar ƙarar, an danganta musu wallafa labaran da suka fito a ranar 22 da 25 ga watan Agusta 2025.
Lauyoyin mai ƙarar sun labaran da jaridar ta wallafa akan Rogo, an rubuta su ne cikin ganganci domin ɓata masa suna.
Kotun ta yi nuni da cewa akwai tuhuma guda biyu a kan Jafar Jafar da Umar:
1. Laifin ɓata suna – mai hukunci ƙarƙashin Sashe na 393 na Dokar Penal Code ta Kano.
2. Take hakkin zaman lafiya – mai hukunci ƙarƙashin Sashe na 114.
Bayan haka kuma, an shigar da wata ƙara ta farar hula a gaban Babbar Kotun Jiha domin neman diyya kan abin da ake zargin ɓata suna.
Sai dai a gefe guda, gwamnatin Kano ta bayyana cewa zarge-zargen na Naira biliyan 6.5 da aka ce an fitar daga baitul-mali ƙarya ne kawai da aka ƙirƙiro da nufin siyasa da ɓatanci.
Kotun ta umarci ‘yan sanda su gudanar da bincike mai zurfi kan yadda aka yi aka wallafa labaran da ake tuhuma da su, tare da tantance dalilin da yasa aka kira wani jami’in gwamnati “ɓarawo” alhali binciken hukumomi kamar ICPC na nan bai kammala ba.