Ƴan Sandan Kano sun kama masu rura rikicin daba a kafafen sada zumunta

0
20

Rundunar ‘yan sandan Kano ta kama wasu matasa biyu da suka shahara a bidiyoyin da suka bazu a kafafen sada zumunta suna ɗauke da makamai.

Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa an cafke Mohammed Isma’il, wanda aka fi sani da Linga daga unguwar Dala, tare da abokinsa Sani Abdulsalam (Guchi). An ce sukan wallafa bidiyo a TikTok da Facebook suna ɗauke da takubba da sanduna suna kuma rura fitina ga matasa.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya jaddada cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani ɗan daba ko wanda ke yada bidiyoyin tashin hankali ba. Ya ce bincike na cigaba kuma za a gurfanar da su a kotu.

Rundunar ta kuma bukaci iyaye da masu kula da yara su sa ido kan halayen ’ya’yansu, tare da godewa jama’a bisa bayanan sirri da suka taimaka wa dasu wajen cafke mutanen dake da laifi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here