Yan bindiga sun kashe jami’in sa-kai da sace mata a Kano

0
7

Wasu ƴan bindiga sun kai hari garin Kafin Maiyaki dake ƙaramar hukumar Kiru a jihar Kano, a tsakar dare inda suka kashe wani jami’in sa-kai sannan suka yi garkuwa da matan wani fitaccen ɗan kasuwar yankin.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun nufi gidan wani mai suna Alhaji Ibrahim Ahmad Rufai, wanda shi ne shugaban ƙungiyar ƴan kasuwar Kafin Maiyaki, inda suka yi awon gaba da matan sa zuwa wurin da ba a sani ba.

A lokacin harin, wani ɗan sa-kai na bijilanti, ya rasa ransa bayan ya yi ƙoƙarin kare al’umma daga harin maharan.

Wani masani kan tsaro, Bakatsine, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis ta hanyar wallafa sakon bayanin hakan a shafin X. 

Har zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa ba kan harin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here