Wani mummunan lamari ya afku a Zaria, Jihar Kaduna, inda rushewar gini a tsakiyar dare ya yi sanadiyyar mutuwar wata uwa da ’ya’yanta uku.
Lamarin ya faru ne a daren Laraba tsakanin ƙarfe 3:30 zuwa 4:00 na safe, lokacin da bangon gida na makwabta da aka ginawa ya rushe sakamakon ruwan sama mai ƙarfi, sannan ya faɗa kan ɗakin da iyalin ke ciki.
Wadanda suka rasa rayukansu sun haɗa da Habiba Nuhu, sai ’ya’yanta Hauwa’u Nuhu da Aina’u Nuhu, da kuma Za’uma.
Mijin Habiba, Mallam Nuhu Dogara, ya tsira da rai bayan ceto shi daga cikin baraguzan ginin, inda aka kai shi asibiti aka yi masa magani kafin daga bisani a sallame shi.
A cewar wani ɗan uwa na mamatan, Mallam Ahmed Ibrahim, al’ummar yankin sun shiga cikin tashin hankali da jimami sakamakon wannan rashi.
Haka zalika, Bello Garba, wanda shi ne mai kula da shiyya ta 1 a Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (SEMA), ya bayyana cewa ba su samu cikakken rahoton faruwar lamarin ba tukuna, amma sun tabbatar da cewa za su tura jami’ai domin gudanar da bincike da kuma tantance barnar da lamarin ya haifar.