Kungiyar ASUU shiyyar Kano ta nemi gwamnatin tarayya ta cika alkawarin dake tsakanin su

0
8

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa (ASUU) shiyyar Kano ta bayyana damuwar ta kan halin da fannin jami’o’i ke ciki a ƙasar nan.

Kungiyar ta bayyana damuwar ta ta, a yau Alhamis, yayin gabatar da wani taron manema labarai.

Taron ya haɗar da jami’o’i kamar su ABU Zaria, BUK, KASU, KUST Wudil, FUD Jigawa, NWU Kano, da Sule Lamido Kafin Hausa.

ASUU ta ce har yanzu akwai matsaloli da dama wanda jami’o’i ke ciki kuma gwamnati ba ta magance ba duk da tattaunawa da dama da aka yi. 

Cikin matsalolin da suka jero sun haɗa da, rashin cika yarjejeniyar ASUU da gwamnatin tarayya wadda aka yi tun n

a shekarar 2009.

2. Rashin samar da ingantaccen kuɗaɗen gudanarwa ga jami’o’in gwamnati.

3. Cin dunduniyar mambobin ASUU a jami’o’in LASU, Prince Abubakar Audu, da FUTO.

4. Rashin biyan bashin albashin malaman da aka yiwa ƙarin kaso 25 zuwa 35.

5. Rashin biyan kuɗin ƙarin girma na tsawon fiye da shekara huɗu.

ASUU ta ce za ta ci gaba da wayar da kai da kuma matsa lamba domin ganin gwamnati ta cika alƙawurran da ta ɗauka wajen inganta ilimin jami’a a Najeriya.

Ƙungiyar ta yi kira ga ɗalibai, iyaye, kungiyoyin farar hula, kafofin yaɗa labarai da sauran ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa da su haɗa kai wajen ceton jami’o’in gwamnati daga rushewa.

Bugu da ƙari, ASUU ta nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro, hauhawar farashin kayayyaki, da ƙaruwar talauci.

Ta ce duk rana ‘yan Najeriya na fuskantar barazanar ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan ta’adda, wanda hakan ya jawo dubban jama’a suka rasa muhallansu da dukiyoyinsu.

Kungiyar ta tunatar da gwamnati cewa babban alhakin ta a tsarin mulki shi ne kare rayuka da dukiyar ‘yan ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here