Gwamnatin tarayya ta ƙara kuɗin yin fasfo

0
12

Hukumar Shige da Fice ta ƙasa (NIS) ta sanar da ƙarin kuɗin neman fasfo, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumba, 2025.

A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, ACI AS Akinlabi ya fitar a ranar Alhamis, an bayyana cewa sabon tsarin kuɗin zai shafi masu neman fasfo a cikin Najeriya kawai.

A cewar sanarwar, sabon kudin zai kasance Naira 100,000 ga fasfo mai shafuka 32 na shekara biyar, yayin da fasfo mai shafuka 64 na shekara goma zai kasance Naira 200,000.

Sai dai sanarwar ta ƙara da cewa, kuɗin neman fasfo ga ‘yan Najeriya da ke ƙasashen waje ba zai sauya ba, inda zai ci gaba da kasancewa $150 ga fasfo mai shafuka 32 na shekara biyar da kuma $230 ga fasfo mai shafuka 64 na shekara goma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here