Gwamnatin Ebonyi ta ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa Naira 90,000

0
10

Gwamnatin jihar Ebonyi ta sanar da ƙarin mafi ƙarancin albashin ma’aikatan gwamnati daga Naira 70,000 zuwa Naira 90,000.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harsuna na jihar, Chief Ikeuwa Omebe, ne ya bayyana haka ranar Alhamis jim kaɗan bayan taron majalisar zartarwa ta jihar.

Omebe ya ce wannan mataki na daga cikin shirin gwamnati na ƙara kula da jin daɗin ma’aikata, inda ya bayyana cewa an fara aiwatar da shi nan take, kuma zai shafi dukkan rukunin ma’aikata.

 Mun riga mun biya kuɗaɗen fansho da gratuti ga waɗanda suka yi ritaya tun daga kafa jihar a 1996 har zuwa yau,” in ji shi.

Ya kuma ƙara da cewa an fara yin tantancewa ga tsofaffin ma’aikatan ƙananan hukumomi domin biyan su hakkokin su nan gaba kaɗan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here