Gwamnatin Habasha ta rattaba hannu kan yarjejeniya da Dangote, domin gina sabuwar masana’antar takin zamani da kuɗin ta ya kai dala biliyan $2.5.
Fira Ministan ƙasar, Abiy Ahmed Ali, ya bayyana cewa wannan babban aiki zai samar da tan miliyan 3 na takin zamani a kowace shekara, lamarin da zai sanya Habasha cikin manyan masu samar da taki a duniya.
Ya ce aikin zai taimaka wajen ƙirƙirar ayyukan yi, rage dogaro da shigo da taki daga waje, da kuma ƙarfafa noman cikin gida domin samar da isasshe.
A baya-bayan nan, Aliko Dangote, ya bayyana cewa cikin shekaru kusan hudu, Afirka za ta iya wadatar da kanta da taki ba tare da dogaro da kasashen waje ba.