Bani da niyyar tsayawa takara a shekarar 2027—El-Rufa’i

0
9

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa ba shi da burin tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa ko wani muƙami a shekarar 2027.

El-Rufai ya yi wannan bayani ne a yayin wani taron siyasa da aka gudanar a Kaduna, inda ya ce dawowar sa cikin harkokin siyasa ba don neman muƙami ba ce, sai don tallafawa shugabanci nagari a Najeriya.

“Asalin shiri na bayan na sauka daga mulkin jihar Kaduna a 2023 shi ne in huta daga siyasa. Amma abubuwan da suka faru kwanan nan suka tilasta min dawowa, ba don kaina ba, amma domin in bayar da goyon baya,” in ji shi.

Sai dai, tsohon gwamnan ya yi tsokaci mai zafi kan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa ta gaza wajen aiwatar da nagartaccen shugabanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here