Babu sauran cin hanci a Najeriya, yanzu komai ya gyaru—Tinubu

0
37
Bola Tinubu
Bola Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ta ɗauka tun bayan hawansa mulki sun kawo gagarumin tasiri, inda ya tabbatar da cewa yanzu haka babu cin hanci da rashawa a harkokin kuɗi da tattalin arzikin ƙasar.

Tinubu ya bayyana haka ne a birnin São Paulo na ƙasar Brazil yayin wata ziyarar aiki da ya kai a wannan makon, inda ya ce Najeriya ta ɗauki sabuwar hanya a ƙarƙashin jagorancinsa.

Idan za’a iya tunawa a yayin da yake ziyarar, Tinubu ya bayyana cewar a yanzu Najeriya ta gyaru don haka akwai wanda duk ƴan ƙasar da suka tafi kasashen waje yin rayuwa su dawo gida don cigaba da yin rayuwa mai inganci.

Sai dai wasu daga cikin al’ummar ƙasar na bayyana cewa har yanzu akwai manyan matsaloli a Najeriya musamman karyewar tattalin arzikin masu ƙaramin ƙarfi, hauhawar farashin kayan masarufi da cin hanci da rashawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here