Ƴan Najeriya sun kashe Naira triliyan 1.3 wajen siyan fetur a wata guda—NMDPRA

0
8
man fetur
man fetur

Hukumar kula da harkokin man fetur ta ƙasa (NMDPRA) ta bayyana cewa, a watan Yuni kaɗai, ‘yan Nijeriya sun kashe kimanin Naira tiriliyan 1.3 wajen sayen fetur domin amfani da shi a sufuri da kuma samar da wutar lantarki.

Bayanan hukumar sun nuna cewa, an rarraba lita biliyan 1.44 na fetur a fadin ƙasar a watan. Legas, Ogun da Babban Birnin Tarayya (Abuja) ne suka fi amfani da man fetur.

Legas ta sha lita miliyan 205.7 (kimanin Naira biliyan 185.1).

Ogun ta sha lita miliyan 88.7 (Naira biliyan 79.8).

Abuja ta sha lita miliyan 77.5 (Naira biliyan 69.8).

Oyo ta sha lita miliyan 72.8 (Naira biliyan 65.5).

Jihohin da suka fi ƙarancin amfani da man sun haɗa da Jigawa (Naira biliyan 8.5) da Ebonyi (Naira biliyan 9.5).

A matakin yanki, Kudu maso Yamma ce ta fi amfani da fetur da jimillar lita miliyan 452.9, wanda darajarsu ta kai Naira biliyan 407.7.

Hukumar ta bayyana cewa dogaro da fetur wajen samar da wutar lantarki, musamman bayan cire tallafin mai shekaru biyu da suka wuce, ya sa kuɗin da al’umma ke kashewa ya tashi zuwa wani sabon mataki da ba a taba gani ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here