Yunwa na ƙara tsananta a Najeriya – Usman Yusuf

0
9

Tsohon shugaban hukumar Inshorar lafiya ta ƙasa NHIS, Farfesa Usman Yusuf, ya ce yunwa ta ƙara kamari a Najeriya, inda ya zargi gwamnoni da rashin faɗa wa Shugaba Bola Tinubu gaskiya, kan halin da a’lumma ke ciki.

Yusuf ya soki shirin tallafin kuɗi na gwamnati, inda ya tambayi inda aka kai biliyan Naira 419 da aka ce an rabawa talakawa. 

Ya kuma ce cire tallafin man fetur ya bawa gwamnoni damar samun karin kuɗi daga gwamnatin tarayya, amma babu wani ci gaba da ake gani.

Ya yi nuni da cewa kashi 80 na matsalolin ƙasar nan gwamnoni ne suka haddasa, musamman ta hanyar hana ƙananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu.

Jama’a na mutuwa da yunwa, amma gwamnoni suna kashe kuɗin al’umma wajen yawon duniya da gina gidaje. Wannan ita ce gaskiyar da ya kamata Shugaban ƙasa ya sani,” in ji Yusuf.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here