Tinubu ya hana fitar da ɗanyen man kaɗanya 

0
10

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar da fitar da ɗanyen man kaɗanya zuwa ƙasashen waje na tsawon watanni shida, domin karfafa sarrafa shi a cikin gida da bunƙasa masana’antar kaɗanya wacce mata ke da kaso mafi rinjaye a cikinta.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, shi ne ya sanar da matakin a Abuja yayin taron masu ruwa da tsaki, inda ya bayyana cewa zai jagoranci kwamitin musamman da aka kafa don ganin an faɗaɗa shirin cikin gaggawa.

Shettima ya ce manufar matakin shine ɗaya darajar Najeriya, samar da ayyukan yi da kuma inganta kuɗaɗen shiga, ba wai kawo cikas ga harkokin cinikayya ba.

Najeriya na cikin manyan ƙasashe masu samar da man kaɗe a duniya, musamman daga jihohin Neja, Kwara da Oyo, inda take da kaso 40% na ɗanyen man kaɗe a duniya. Amma duk da haka tana da kaso 1% ne kacal a kasuwar da darajarta ta kai dala biliyan 6.5.

Rahotanni sun nuna cewa sama da tan 90,000 na man kaɗe ake fitarwa ba bisa ƙa’ida ba a kowace shekara, abin da ke rage ƙarfin masana’antun cikin gida.

A cewar Shettima, matakin zai iya samar da kusan dala miliyan 300 a shekara nan gaba, tare da nufin ninka hakan zuwa shekarar 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here