Son cigaban ƙasa ne yasa PDP bayar da tikitin shugaban ƙasa ga kudu–Gwamnan Bauchi

0
12

Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana cewa matakin jam’iyyar PDP na yanke hukuncin bayar da tikitin takarar shugaban ƙasa na 2027 zuwa yankin kudu, wata sadaukarwa ce domin haɗin kai da zaman lafiya a jam’iyyar da ƙasa baki ɗaya.

A ranar Litinin, kwamitin gudanarwar PDP na ƙasa (NEC) ya amince da tsarin rabon mukamai inda kujerar shugaban jam’iyya za ta ci gaba da kasancewa a arewa, yayin da tikitin shugabancin ƙasa aka miƙa shi ga kudu. Wannan matakin ya cire damar fitowa takara ga manyan ‘yan siyasar arewa ciki har da Bala Mohammed.

Da yake jawabi ga manema labarai a Bauchi, Bala ya ce, na matuƙar gamsuwa da wannan matsaya saboda na kasance cikin waɗanda suka amince da  hakan.

 Mun yanke shawara ta haɗin kai domin gudanar da babban taron mu a Ibadan ranar 15 ga Nuwamba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here