Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 104,000 ga ma’aikatan gwamnatin jihar.
Uzodimma ya bayyana hakan ne yayin wani taro da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago a gidan gwamnati dake Owerri da yammacin Talata. Wannan sabon albashi ya zo ne bayan samun ƙarin tsohon mafi ƙarancin albashi daga Naira 76,000 zuwa Naira 104,000.
Haka kuma, albashin likitoci ya tashi daga Naira 215,000 zuwa Naira 503,000, yayin da na malamai a manyan makarantu ya tashi daga Naora 119,000 zuwa Naira 222,000.
A cewar gwamnan, gwamnatin jihar ta ga ƙalubale iri-iri tun bayan da ta hau mulki a shekarar 2020, ciki har da rashin tsaro, annobar COVID-19 da matsalolin tattalin arziki da suka biyo bayan cire tallafin mai.
Shugaban kungiyar Kwadago ta kasa (NLC) a jihar, Uchechigemezu Nwigwe, ya yaba da wannan ƙarin albashi, yana mai cewa, yau babu wani ma’aikacin Imo da zai ce gwamnati ba ta yi masa adalci ba.