Hisbah ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776, a Kano

0
14

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a shekarar 2024, ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776, tare da warware rikicin aure 621. Haka kuma hukumar ta tara kuma ta raba kuɗaɗen tallafi da bashin da aka gaza biya da ya kai Naira miliyan 212,334,839.

Kwamandan rundunar, Sheikh Amin Ibrahim Daurawa, ya ce tun bayan zuwan Gwamna Abba Kabir Yusuf a ranar 29 ga Mayu, 2023, an inganta harkokin Hisbah domin ciyar da ayyukanta gaba.

Ayyukan da hukumar ta gudanar sun haɗa da:

  • Auren Gata ga ma’aurata 3,800.
  • Horon ƙwarewa ga jami’an Hisbah 1,000.
  • Rabon kayan tallafi ga marayu, gwauraye da gajiyayyu.
  • Taimakawa wajen aikin Hajji daga Kano zuwa Saudiyya.

A halin yanzu, rundunar tana da fiye da jami’ai 4,000 da ke aiki a kananan hukumomi 44 na jihar, tare da sassan ayyuka da dama ciki har da bangaren mata karkashin jagorancin Dr. Khadija Sagir Suleiman.

Gwamnatin Kano ta bayyana shirin kafa makarantar horar da jami’an rundunar, ƙara albashi da tsarin ritaya ga jami’an Hisbah, sabbin kayan aiki da kuma gina sabuwar hedikwatar hukumar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafawa Hisbah don tabbatar da adalci, zaman lafiya da ɗorewar ɗabi’u masu kyau a Kano.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here