Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin mutum 11 domin binciken siyar da mayankar dabbobi da gwamnatin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta yi a yankin Chalawa.
Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya ce kwamitin zai binciki yadda aka gudanar da cinikin filin da tantance ko an bi doka da ƙa’idoji.
Kwamitin zai kuma gano masu hannu a siyarwar, gano kadarori ko kuɗaɗen gwamnati da suka ɓace, da bayar da shawarwari kan hukuncin da ya dace a ɗauka. Haka kuma zai bada shawarwari kan yadda za a hana faruwar irin wannan matsala a gaba tare da shirin kafa sabuwar mayaka ta zamani.
Kwamitin, ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano, Barr. Muhuyi Magaji Rimin Gado, zai mika rahoton bincikensa cikin makonni uku.