Cutar Kwalara Ta Kashe Mutane a Zamfara, Sama da 200 Sun Kamu

0
7

Cutar kwalara ta barke a wasu ƙananan hukumomin jihar Zamfara, inda ta hallaka aƙalla mutum bakwai a Gumi da Bukkuyum. Rahotanni sun nuna cewa fiye da mutum 200 aka kwantar a asibitoci, lamarin da ke jefa jama’a cikin fargaba.

Hon. Sulaiman Abubakar Gumi, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Gumi/Bukkuyum, ya shaida cewa cutar ta fara bayyana tun daga ranar 10 ga watan Agusta, 2025. A cewarsa, a ƙaramar hukumar Bukkuyum kaɗai mutum 157 aka kwantar, yayin da a Gumi an kwantar da mutum 24 a Unguwar Gamji.

Ya bayyana cewa a Birnin Waje ma, duk da cewa ba a samu rahoton bullar cutar da wuri ba, an yi asarar rayuka bakwai.

Ya yi gargadin cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, barkewar cutar na iya zama annoba. Ya ce mafi yawan matsalar ta samo asali ne daga halin da ‘yan gudun hijira da ke Bukkuyum suka tsinci kansu a ciki, inda ruwan sama ya lalata sansanoninsu, ya tilasta musu yin bahaya a wuraren da ba su dace ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here