Ƴan arewa sun tafka asara a kasuwar jihar Lagos

0
12

‘Yan kasuwar Alaba Rago da ke karamar hukumar Ojo a jihar Legas sun nemi gwamnatin jihar ta biya su diyya bisa asarar dukiyoyin da suka yi, bayan rusau da jami’an gwamnati suka gudanar a kasuwar.

Kasuwar, wadda mafi yawan ‘yan kasuwarta daga arewacin Najeriya suke, ta fuskanci mummunan rusau tsakanin ranar Lahadi 17 zuwa Laraba 20 ga watan Agusta, 2025. A cewar ‘yan kasuwar, asarar ta kai biliyoyin naira, inda aka rusa shaguna, wuraren ajiya da kuma wuraren sana’o’i ba tare da an ba su damar kwashe kayansu ba.

Alhaji Adamu Katagum, Wazirin Sarkin Alaba Rago, ya bayyana cewa: “An rusa shagunan sayar da kayan abinci, nika, da ma gidajen ajiya. Asarar da aka yi ta kai biliyoyin kudi, kuma muna neman diyya domin gwamnati ta biya mu hakkokinmu.”

Shi ma wani dan kasuwa, Alhaji Bala Kofar Sabuwa, ya yi zargin cewa jami’an gwamnati sun shiga kasuwar da sunan aikin titi amma daga bisani suka kwace kayayyaki tare da rushe shaguna, abin da ya jawo jama’a da dama suka shiga halin kunci.

A bara, gwamnatin jihar ta yi yunƙurin irin wannan rusau amma Sarkin Hausawan Legas, Alhaji Aminu Yaro Dogara, da tawagarsa sun sa baki aka dakatar. Sai dai a wannan karo, gwamnati ta ci gaba da aikin da nufin, a cewarta, zamanantar da manyan kasuwanni take yi domin su yi daidai da tsarin zamani.

‘Yan kasuwar sun yi gargadin cewa idan ba a biya su diyya ba, za su ɗauki matakan doka don kare hakkokinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here