Zamu cigaba da shari’a akan Abdullahi Ibrahim Rogo–ICPC

0
10

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da gangogin su ta ƙasa ICPC, tace zata ɗaukaka akan dakatarwar da kotu tayi mata, akan kokarin binciken zargin almundahanar kuɗaɗe da yawan su ya zarce Naira biliyan 6.5 daga daraktan tsare-tsaren fadar gwamnatin Kano, Abdullahi Ibrahim Rogo.

Daya daga cikin jami’an hukumar ICPC, Hassan Salihu, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da BBC Hausa, dangane da halin da ake ciki ta fannin zargin.

Yace da farko hukumar ta aikewa Rogo, da wasikar gayyata amma ya rika neman uzuri daga bisa ni ya kai su kotu inda aka hana binciken sa, ko kama shi.

Sai dai jami’in yace sun samu umarnin kotu akan kwato Naira biliyan 1 da miliyan 109, wanda wannan adadi baya daga cikin Naira biliyan 6.5 da ake zargin Rogo, da wawure wa, yana mai cewa bincike ne zai bayyana gaskiya akan zargin da ake yi, saboda an samu Naira biliyan 1 da miliyan 109, daga wasu kamfanoni da suke ma’amala da wanda ake zargin.

Idan za’a iya tunawa dai bayan fitar da wannan zargi, gwamnatin Kano ta musanta hannun jami’in nata a aikata cin hanci da rashawa, kamar yadda kakakin gwamnan Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana, sannan yace wata manaƙisar siyasa ce ta sanya zargin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here