’Yan Sanda Sun Fara Binciken Jami’an KAROTA Bisa Zargin Aikata Sata

0
11

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta fara bincike kan wasu jami’an Hukumar Kula da Zirga-zirgar ababen hawa ta Kano (KAROTA) bisa zargin yin duka da kuma satar kayayyakin wani mutum.

Wani lauya a Kano mai suna Ahmad Sani Bawa, ne ya kai ƙara yana zargin wani jami’in KAROTA, Abdulwahab Abdullahi, da wasu abokan aikinsa da kwace agogonsa na hannu, yi masa duka da kuma satar masa Naira 950,000.

Lauyan ya kai ƙarar ne ta hannun tawagar lauyoyi 10 da Barrister Fengak Obadiah Gokir ke jagoranta, inda suka rubuta takardar ƙorafi ga Kwamishinan ’Yan Sanda na Kano, Ibrahim Adamu Bakori.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da karɓar ƙorafin, inda ya ce wanda ya kai ƙarar ya riga ya bayar da bayanai, sannan kuma an gayyaci jami’an da ake zargi domin su bada nasu bayanin.

A nasa ɓangaren, kakakin KAROTA, Abubakar Sharada, ya tabbatar da cewa hukumar ta samu labarin ƙorafin, tare da tabbatar da cewa za a gudanar da bincike cikin gaskiya da adalci kafin daukar mataki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here