Jirgin Ƙasan Abuja Zuwa Kaduna ya yi hatsari

0
13

Wani jirgin ƙasa da ke tafiya daga Abuja zuwa Kaduna ya yi hatsari a safiyar Talata, inda wasu daga cikin taragon jirgin suka kife, lamarin da ya jefa fasinjoji cikin tashin hankali da firgici.

Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safe, jim kaɗan bayan jirgin ya bar Abuja. Shaidu sun ce fasinjoji sun rika yin gudun ceton ransu cikin rudani da firgici.

A halin yanzu ba a tabbatar da adadin waɗanda suka jikkata ba ko kuma mutanen da suka rasa rayukansu. Sai dai jami’an tsaro sun isa wajen domin taimakawa wajen ceto.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here