Gwamnati ta dakatar da zirga-zirgar jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna

0
14

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC) ta dakatar da jigilar jiragen ƙasa a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna har sai wani lokaci.

Shugaban hukumar, Kayode Opeifa, ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a Abuja, jim kaɗan bayan hatsarin da ya faru a hanyar, wanda ya janyo hatsarin jirgin kasa bayan saukar sa daga layin dogo a tsakanin Abuja zuwa Kaduna.

Ya ce a halin yanzu, ma’aikatan NRC tare da jami’an hukumar binciken sufuri ta ƙasa (NSIB) da sauran hukumomin tsaro suna ci gaba da gudanar da bincike a wurin da lamarin ya auku.

Opeifa ya musanta zargin cewa jiragen ƙasan ba su da inganci, inda ya tabbatar da cewa an fara mayar da kuɗaɗen tikiti ga dukkan fasinjojin da abin ya shafa.

Haka kuma, ya ce hukumar ta karɓi wasu daga cikin fasinjojin da ke cikin jirgin a tashar Asham da kuma tashar Idu domin kula da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here