Fiye da Mutane 10,000 Sun Rasa Rayukan su a Shekaru Biyun Mulkin Tinubu–Obi

0
8

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, ya sake nuna damuwa kan yadda ake ta kashe-kashe a sassan Najeriya ba tare da ƙarewa ba.

Obi ya ce, bisa ga rahoton kungiyar kare hakkin dan Adam ta, Amnesty International, mutane sama da 10,000 ne ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da sauran kungiyoyin ta’addanci suka hallaka a cikin shekaru biyu kacal na mulkin Shugaba Bola Tinubu.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Obi ya bayyana cewa Najeriya ba ta cikin yaƙi, amma adadin mutanen da aka kashe ya kai kusan irin wanda aka rasa a Ukraine, wadda take cikin yaƙi na gaskiya.

Ya kuma ambaci harin da aka kai kwanan nan a Okigwe, Jihar Imo, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da wasu da ba a san inda suke ba, inda ya ce hakan alama ce ta tsananin matsalar tsaro.

Obi ya ƙara da cewa a mako guda kacal, fiye da mutum 50 aka kashe a masallaci a Katsina, sama da mutum 60 aka sace a jihar ɗaya, sannan a Mangu, Jihar Filato, aka kashe manoma 15 tare da tilasta iyalai 200 su bar gidajensu.

Ya ƙara nanata cewa lokaci ya yi da shugabanni za su tashi tsaye wajen samar da sabuwar Najeriya mai adalci da tsaro ga kowa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here