ASUU ta shirya fara yajin aikin da a’a  taɓa yin Irin sa ba

0
13

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa (ASUU) ta bayyana cewa ta shirya tsaf domin shiga wani yajin aiki mafi girma a tarihin ta, har sai gwamnatin tarayya ta cika dukkan yarjejeniyoyin da aka kulla a shekarar 2009.

Shugaban ASUU reshen Jami’ar Calabar, Dr. Peter Ubi, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a Calabar, inda ya ce gwamnati ta gaza aiwatar da yarjejeniyoyin da za su inganta ilimi a jami’o’i.

Ya bayyana cewa idan har kwamitin koli na ASUU ya amince bayan taron da za su yi a ranar 28 ga watan Agusta, za a shiga yajin aikin nan take.

Daga cikin bukatun kungiyar akwai:

Sake duba yarjejeniyar 2009

Samar da ingantaccen kudaden gudanar da jami’o’i

Farfado da jami’o’i ta fannin kayan aiki da gina sabbin dakunan karatu da gwaje-gwaje

Biyan kashi 25-35% na karin albashi da gwamnati ta yi alkawari

Biyan watanni uku na bashin albashi

Da kuma biyan kudaden karin matsayi (promotion arrears) da malaman ke bi sama da shekaru hudu.

Dr. Ubi ya kara da cewa gwamnati ta saba yin alkawura amma ta gaza cika su, abin da ya tilasta ASUU amfani da yajin aiki a matsayin karshen hanya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here