An yiwa ƙananun yara biyu kisan gilla a Kano

0
12

Rahotanni daga jihar Kano sun tabbatar da wasu munanan al’amura guda biyu da suka girgiza al’umma.

A Karamar Hukumar Rimingado, wani ƙaramin yaro mai suna Junaidu Ibrahim, ɗan shekaru 7, ya rasa ransa bayan wasu ɓata-gari da ba a san ko su waye ba suka yi masa yankan rago a kauyen Zangon Dan Abdu. Mahaifinsa, Ibrahim Aliyu, ya shaida cewa a ranar Lahadi aka sanar da shi an tarar da ɗansa cikin jini a gona, sai dai daga baya aka tabbatar da cewa an yanka masa wuyan ne.

Mai unguwar yankin, Ibrahim Chiroma, ya ce duk da cewa ba a cire wani sashi daga jikinsa ba, akwai zargin cewa masu laifin sun tatse jininsa.

A wani lamari mai kama da haka a ranar Asabar, an samu wata yarinya mai shekaru 13, Fatima Sule, da aka kashe a unguwar Dandishe Yamma, dake Dala.

 Rahotanni sun nuna cewa hakan ya faru ne a lokacin da mahaifiyarta ta fita, amma da ta dawo sai ta tarar da ita rataye a mace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here