Wasu jihohi ne ke ta’azzara matsalolin Kano–Sarkin Kano na 15

0
6

Sarkin Kano, na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana cewa wasu daga cikin matsalolin tsaro da ake samu a Kano ba su samo asali daga cikin jihar ba, sai dai daga wasu jihohin makwabta.

Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana haka ne yayin da yake karɓar tawagar kungiyar Arewa Pirth Initiative karkashin jagorancin shugaban ta, Alhaji Aminu Adam.

Ya jaddada cewa wajibi ne matasa su dage wajen neman hanyoyin da zasu taimaka don sauƙaƙa rayuwa da kuma samun ayyukan yi, yana mai cewa zasu ci gaba da bayar da goyon baya ga duk wani yunƙuri da zai kawo cigaba.

Tun da farko, shugaban kungiyar Arewa Pirth Initiative, Alhaji Aminu Adam, ya ce sun ziyarci Alhaji Aminu Ado Bayero, domin neman shawarwari wajen cimma manufofinsu na wayar da kan matasa kan tarbiyya da dogaro da kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here