Jam’iyyar PDP ta amince ta bayar da tikitin takarar shugabancin kasa na shekarar 2027 zuwa yankin Kudu.
Shugabannin jam’iyyar sun dauki wannan mataki ne a taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) da aka gudanar a ofishin jam’iyyar dake Abuja ranar Litinin.
Wannan mataki na iya sauya taswirar siyasar PDP, inda ake sa ran manyan ‘yan siyasar kudu za su fara shiri domin neman tikitin.