Haƙurin ƴan arewa ya kusa ƙarewa—ACF

0
1

Kungiyar tuntuɓa ta arewa (ACF) ta bayyana damuwarta kan halin da ake ciki a yankin Arewa, tana mai cewa lokaci ya yi da shugabanni da al’umma za su tashi tsaye wajen fuskantar matsalolin tsaro, tattalin arziki da muhalli da ke kara tabarbarewa.

Shugaban kungiyar, Mamman Osuman, ya bayyana hakan ne yayin taron kwamitin koli na 78 na kungiyar da aka gudanar a Kaduna ranar Alhamis, 21 ga Agusta, 2025.

A cewarsa, “Yanzu ba lokaci ne na yin shiru da kame baki ba yayin da ake ci gaba da kashe rayuka, sace mutane, da lalata al’umma a Arewa. Mun rasa matasa, yara, mata da tsofaffi sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda, ambaliya, da miyagun bata-gari. Wannan babban abin damuwa ne, dole mu tashi tsaye da addu’a da hadin kai.”

A yayin tattaunawa da BBC, mai ba da shawara ga kungiyar, Bashir Hayatu Gentile, ya ce taron ya mayar da hankali ne kan matsalolin tsaro da rayuwar al’umma. Ya ce ACF ta yanke shawara cewa lokaci ya yi da al’umma za su matsa wa gwamnati domin ta dauki matakai na musamman wajen dakile matsalar.

Gentile ya kara da cewa, “Babu abin da ya fi damun Arewa yanzu sama da matsalar tsaro. Dole mu matsa wa gwamnati ta dauki sabbin dabaru saboda hakurin Arewa ya kusa karewa.”

Ya kuma nuna damuwa kan rahoton da Amnesty International ta fitar, inda aka bayyana cewa a cikin shekara biyu na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, mutane 10,217 aka kashe a Arewacin Najeriya kadai, baya ga daruruwan da ake sacewa a kullum.

Gentile ya ce lamarin da ya fi girgiza al’umma shi ne na baya-bayan nan a Malumfashi, jihar Katsina, inda aka kai hari cikin masallaci a lokacin sallar asuba, aka kashe sama da mutum 27 tare da kona wasu.

“Abin takaici shi ne, har zuwa yau babu wani jami’in gwamnati da ya fito ya karyata wannan rahoto. Wannan ya nuna cewa lokaci ya yi da tsarin da ake bi yanzu ya sauya.” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Logged in as Ismail Ishaq-Ibrahim. Log out?

Please enter your comment!