Gwamnatin Kano Za Ta Horar da Matasa Miliyan 1.5 Kan Fasahar Sadarwa

0
1

Hukumar Ci gaban Fasahar Sadarwa ta Jihar Kano (KANSITDA) ta bayyana cewa tayi haɗin gwiwa da ƙungiyar KALM Community Initiative domin koyar da matasa miliyan 1.5 ƙwarewar zamani ta fannin fasahar sadarwa (digital skills).

Daraktan Hukumar, Dakta Bashir-Abdu Muzakkari, ne ya bayyana haka yayin wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a gefen wani taron da ƙungiyar KALM ta shirya a Zariya.

Ya ce wannan shirin wani ɓangare ne na manufar gwamnati ta cigaban tattalin arzikin harkokin fasahar zamani, daga shekarar 2025 zuwa 2027.

Muzakkari ya bayyana cewa an riga an fara aikin gwaji inda aka horar da matasa 150,000, yayin da wasu 1,150 suka kammala karatu daga Cibiyar Kasuwanci ta Jihar Kano da kuma Cibiyar Fasahar Sadarwa ta Kano. Haka kuma gwamnati na shirin yada shirin KALM a manyan makarantu da jami’o’i a jihar.

A nata ɓangaren, wadda ta kafa ƙungiyar KALM, Hajiya Aisha Muhammad, ta ce manufar ƙungiyar ita ce buɗe ƙofofin cigaba ga matasan Najeriya ta hanyar fasahar zamani. 

LEAVE A REPLY

Logged in as Ismail Ishaq-Ibrahim. Log out?

Please enter your comment!