Gwamnatin Kano ta yi gargadi akan masu sace kayayyakin ta da sunan gwan-gwan

0
1
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Gwamnatin Kano ta yi gargadi akan masu sace kayayyakin ta da sunan gwan-gwan

Gwamnatin jihar Kano ta yi gargaɗi mai tsanani ga matasa da kuma masu kasuwanci kan satar kayayyakin gwamnati irin su ƙarafan tituna, fitilu da wayoyin lantarki.

Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bada umarni na musamman ga Ma’aikatar Ayyuka tare da hukumomin tsaro domin ƙara sa ido kan wannan matsala. Haka kuma, an gudanar da taro da shugabannin masu sana’ar ƙarafa a jihar domin tattaunawa kan yadda za a kawo ƙarshen satar kayayyakin gwamnati don siyar da su a matsayin gwan-gwan.

Kwamishinan Ayyuka na jihar, Injiniya Marwan Ahmed, ya bayyana cewa, idan ba a sayi waɗannan kayayyaki daga hannun barayi ba, to babu wanda zai sace su. Duk wanda aka kama, ko mai satar kayayyakin ko mai siye, duka za a ɗauki mataki mai tsauri a kansu saboda duk ɓarayi ne.

Ya kuma yi kira ga iyaye, shugabannin unguwanni da ‘yan kasuwa da su sa ido kan ‘ya’yansu tare da guje wa sayen kayayyakin gwamnati daga hannun bata gari.

LEAVE A REPLY

Logged in as Ismail Ishaq-Ibrahim. Log out?

Please enter your comment!