Gwamnatin Jihar Kano ta karyata rahoton da ya zargi Daraktan Tsare-tsare na Fadar Gwamnati, Alh. Abdullahi Ibrahim Rogo, da karkatar da sama da naira biliyan 6.5 daga baitul-mali.
A wata sanarwa, da Kakakin gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar gwamnatin ta ce duk kudaden dake fita daga asusun ta ana gudanar da su ne bisa kasafin kudi, ba tare da wani jami’i ya mallaki ikon kashe kuɗi yadda ya ga dama ba.
Sanarwar ta bayyana cewa zargin da aka wallafa a Daily Nigerian ya samo asali ne daga adawa da ke ƙoƙarin bata sunan gwamnati kafin 2027, tare da jaddada cewa Rogo mutum ne mai gaskiya da amana.
Gwamnatin ta kuma tunatar da yadda tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kashe fiye da naira biliyan 20 cikin watanni uku kacal a shekarar 2023, tana mai cewa mutanen Kano sun san irin cin hanci da rashawa da taƙaita dukiya da aka yi a baya.
Wannan zargi ƙarya ce ta siyasa. Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ba za ta bar ƙoƙarin bata sunan jami’anta ya yi tasiri ba,” in ji sanarwar.
Gwamnati ta ce za ta ci gaba da gudanar da mulki cikin gaskiya da rikon amana, tare da gargadin masu yada ƙarya da siyasar bata suna.