Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da kwamiti mai mambobi 26 daga hukumomi daban-daban domin shirya bukukuwan cikar Najeriya shekara 65 da samun ’yancin kai.
Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya jagoranci bikin kaddamarwar a yau Litinin.
A cewarsa, kwamitin zai tsara yadda bikin ranar 1 ga Oktoba 2025 zai gudana tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro, inda aka samu wakilcin manyan jami’an tsaro daga sassa daban-daban na jihar da kuma na ƙasa baki ɗaya.
Kwamared Waiya ya bayyana cewa bikin bana zai bambanta da na baya, duba da yadda za a samu manyan baki daga hukumomin tsaro da sauran bangarori. Ya ƙara da cewa za a gudanar da addu’o’i na musamman da kuma shirye-shiryen wayar da kan matasa kan muhimmancin kishin ƙasa kafin ranar taron.
Daga cikin hukumomin da ke cikin kwamiti akwai ’yan sanda, rundunar tsaron farin kaya (Civil Defence), sojoji, hukumar Hisba da wasu hukumomin tsaro daban-daban.