Na yi baƙin cikin yadda jihohin Kano da Sokoto, zasu inganta rayuwar al’ummar jihar Lagos–Salihu Tanko Yakasai

0
11

Ɗaya daga cikin ƴan siyasa, masu sharhi akan al’amuran yau da kullum, Salihu Tanko Yakasai, ya yabawa gwamnatin Lagos bisa kokarin inganta harkokin tattalin arzikin ta, da kuma takaicin yadda jihohin arewa suka gaza yin irin haka, biyo bayan bude wani kamfani da jihar Lagos tayi na sarrafa fata domin samar da jakunkuna, takalma da sauransu.

Ga cikakken bayanin da yayi a shafin sa na Facebook, a safiyar yau Lahadi;

A jiya, uwargidan shugaban kasa Remi Tinubu ta kaddamar da kamfanin sarrafa fatar dabbobi domin yin takalma, jaka, belt da makamantan su. Gwamnatin jihar Lagos ce ta samar da Kamfanin, kuma an kiyasta cewa za’a dau maaikata kimanin dubu goma na dindindin. Sannan kuma kimanin mutum dubu dari da hamsin (150,000) ne zasu ci moriyar wannan kamfanin. Sannan jihar Lagos zata na samun kimanin $250Million duk shekara na kudin shiga ta dalilin wannan kamfanin da ta samar. 

A hannu daya, ina yabawa jihar Lagos bisa wannan hangen nesa da tai wa kanta, a dayan hannun kuma, takaici ne ya ke nema ya shake ni, duba da cewa jihohin Kano da Sokoto, kusan su suke samar da fatar da wannan kamfanin zai amfani da su wajen samar da wadannan tagomashin arzikin ga jihar Lagos, amma su jihohin namu biyu na Arewa, basu samar da irin wannan kamfanin ba.

Kai hasali ma, jihohin Kano da Sokoto, kusan su ke samarwa da kasashen turai (irin su Italy, da Spain) fatar da suke yin takalma da jakunkuna na alfarma kamar su takalmin Bertozzi, ko jakar Gucci, wanda masu kudin mu suke zuwa su siyo su da tsada. Wannan al’amari ba wai sabon abu ne ba, kusan tun kafin zuwan turawa aka san jihar Kano da samar da fata ga kasar Morocco, wadda ita ma take siyarwa da turawa. 

Na san a Kano, akwai kamfanonin jima wato tannery, wanda suke gyara fatun, su shirya su, domin a fitar da su. Amma ba mu da katafaren kamfanin da zai sarrafa fatar zuwa kayan alfarma kamar yadda Lagos zata fara. 

Lokacin Gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje, da ni aka je China, garin Shandong, domin tattaunawa da kamfanin fata da na tufafi wato textile, kuma bayan dawowar mu, yan china din sun turo tawaga mai karfi, inda suka zo Kano, domin duba yiyuwar saka hannun jari, amma babbar matsalar da ta hana wannan alamari faruwa shine rashin wutar lantarki. Harkar fata da textile abu ne mai bukatar wutar lantarki kuma jihar Kano bata da shi a wadace, sannan policy din gwamnatin taraiya a lokacin bai lamunce jihohi su gina ba, idan ma sun gina toh sai dai su dora wutar lantarkin akan national grid a rabawa kasa baki daya, wanda wannan ne ya hana kamfanunuwa da dama, kin saka hannun jari a harkar lantarki a jihohi. Zan iya tunawa, Ganduje ya bada fili ga kamfanunuwa uku (Dangote, da Blackrhino wanda Sarki Sanusi ya kawo su, da kuma wani kamfanin chinese) domin samar da wutar lantarki mai amfanin da hasken rana wato Solar, mai karfin megawatts dari (100MW ko wacce, total 300MW kenan). Sai karshen gwamnatin Buhari ne, aka sahalewa jihohi damar gina kamfanin samar da wuta, wanda zasu iya amfani da shi a jihar su. Ina fata Gwamna Abba Kabir zai farfado da zancen wannan wutar solar ko da ta Dangote ce, da ta Blackrhino ta Sarki Sanusi, ya kuma zage dantse domin ganin ya samar wa da jihar Kano wuta sosai, domin farfado da masana’antun mu.

Damuwa ta guda daya ce akan wannan kamfanin da jihar Lagos ta kafa. Ire iren wadannan abubuwan, sune arzikin arewa, idan ba ma tsayawa muna gina su, toh daya bayan daya haka Gwamnonin jihohin Lagos ko Ogun ko Fatakwal zasu dinga yi, kuma suna zuwa arewa suna kwasar raw materials, suna kai wa jihohin su, su sarrafa su dawo mana da shi mu siya. Kaga kenan su sun samar wa mutanen su aikin yi, mu mun zama yan kamasho, yan cima zaune. Zasu kuma samu kudin shiga, sannan tattalin arzikin jihohin su zai kara habaka. Mu kuma gwamnonin mu na arewa, a bar su da rabon jajayen awaki. 

Muna da matasa masu hazaka a kofar wambai, suna nan suna kera takalma wanda idan ba’a fada ma ba, sai ka ce daga turai aka kawo su. Ina ma ace Kano zata samu irin wannan kamfanin na Lagos, ta kwaso yan kofar wambai ta ce musu su kure bajintar su a gun. Kai ka san cewa wallahi baza su ba wa Kanawa kunya ba. Toh amma ina, haka zamu ci gaba da cizon yatsa, muna ganin yan uba suna ci gaba, mu kuma muna tunkaho da tutiya da mun fi yawa, mun fi iya siyasa. Amfani da damar siyasar kuma, mun barwa yan uba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here