Gwamnatin jihar Kano ta yi kira da a kara yawan rumfunan zabe a fadin jihar, domin saukaka wa masu kada kuri’a da kuma rage cunkoson da ake fuskanta yayin zabe.
Shugaban kwamitin wayar da kan al’umma kan muhimmancin mallakar katin zabe, kuma kwamishinan yada labarai na jihar, Comr. Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya yi wannan kira yayin wata ziyarar da ya kaiwa shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) reshen Kano, Amb. Abdu Zango.
Waiya ya bayyana cewa sabbin gundumomi da unguwanni da aka samar a jihar na bukatar a shigar da su cikin jadawalin hukumar zabe, tare da kirkirar sababbin rumfunan zabe domin rage cunkoso da ake samu a wasu wurare. Ya kuma jaddada kudirin gwamnatin Kano na ci gaba da zama jihar da tafi kowacce jiha yawan masu kada kuri’a a Najeriya.
A nasa jawabin, shugaban INEC na Kano, Amb. Abdu Zango, ya bayyana cewa sama da katin zabe 360,000 na nan a ofisoshin hukumar, wadanda masu su ba su karba ba. Ya bukaci kwamitin da ya taimaka wajen fadakar da jama’a kan muhimmancin karbar katin nasu kafin zabe.