Gwamnatin Kano Ta Karyata Sayar da Fom ɗin Neman Aiki

0
9
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Hukumar Kula da Ma’aikatan Jihar Kano ta bayyana cewa ba ta taɓa bayar da izinin sayar da fom ɗin neman aiki ba, duk da wata jita-jita da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa ana sayar da fom ɗin neman aiki ga masu neman shiga aikin gwamnatin Kano.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a na hukumar, Musbahu Aminu Yakasai, ya fitar, ya ce wannan magana karya ce baki ɗaya, don haka jama’a su yi watsi da ita.

Hukumar ta ja hankalin al’umma da su rika dogaro da ingantattun tashoshin samun bayanai na gwamnati kawai wajen batun daukar ma’aikata da sauran ayyuka na hukumar.

Sanarwar ta kara da cewa hukumar za ta ci gaba da bin hanyoyin gaskiya, tsabta da bin ƙa’ida a duk wani shirin daukar ma’aikata, tare da gargadin cewa duk wanda aka kama yana yaudarar jama’a da sunan hukumar za a gurfanar da shi a gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here