Daliban makarantar firamare a unguwar Turawa da ke karamar hukumar Karaye, Jihar Kano, na gudanar da karatu a fili karkashin bishiyu sakamakon rushewar mafi yawan ginin makarantar su.
Rahotan jaridar Solacebae, ya nuna cewa daga cikin dakunan karatu guda shida da makarantar ke da su, uku sun rushe gaba daya, biyu kuma babu rufi, yayin da daya tilo da ke aiki bai da bene, lamarin da ke tilasta yara su zauna a kasa suna karatu.
Malaman makarantar sun bayyana cewa idan aka samu ruwan sama, dole su rufe makaranta domin tsaron dalibai, abin da ke kawo tsaiko ga tsarin koyarwa.
Iyayen ɗalibai a yankin sun nuna damuwa matuka kan wannan hali, suna kiran gwamnati da ta gaggauta daukar mataki. “Yaran mu ba za su iya yin gogayya da sauran yara a birane ba idan suna karatu a karkashin itatuwa,” in ji wani uba mai suna, Malam Haruna Ibrahim.
Shugaban Kungiyar Iyaye da Malamai (PTA), Malam Sulaiman Idris, ya ce sun yi ta rubuta korafe-korafe ga hukumomi, amma babu martani. Shugaban al’ummar yankin, Nazifi Ibrahim Muhammad, ya roki gwamnatin jihar Kano da kungiyoyin tallafi da su taimaka wajen sake gina makarantar.
A martaninsa, Kwamishinan Ilimi na jihar, Alhaji Ali Bukar Makoda, ya ce gwamnatin jihar ta gaji gine-ginen makarantu da dama a lalace, kuma tana ci gaba da gyarawa.