Tinubu Ya Tallafa wa Kiristoci, sai dai Musulmai Na Kukan Tsadar Zuwa Hajji– Salisu Kofar Wambai

0
13

Wani masanin harkokin siyasa daga Kano, Salisu Uba Kofar Wambai, ya zargi Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) da rashawa da cin hanci, yana mai cewa alhazai Musulmi na fuskantar matsanancin tsadar Hajji a wannan shekara.

A cewarsa, yayin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rage kuɗin tafiyar ibada na Kiristoci da kashi 50%, farashin aikin Hajji ya kai Naira miliyan 9 lamarin da ya ce ya hana dimbin Musulmi samun damar sauke wannan rukuni na addini.

Wambai ya bayyana cewa NAHCON, wadda ke karkashin jagorancin Musulmi, ta gaza kare muradun alhazai, maimakon haka tana amfani da tsarin biyan kuɗi na Naira miliyan 8.5 tun kafin sanar da ainihin farashi, abin da ya kira dabarar zamba.

Ya kuma caccaki wasu malaman addini da suka yi shiru kan wannan batu, duk da cewa sun amfana da kujerun aikin Hajji kyauta a baya, yana mai cewa: “An mayar da ibadar Hajji kasuwa ta zamba, inda masu mulki ke cin moriyar talakawa.”

Ya yi kira ga gwamnati da ta tsaftace hukumar NAHCON, tare da samar da shugabanni masu tsoron Allah da za su kare hakkokin Musulmai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here