Jam’iyyar PDP ta tabbatar da cewa tana nan daram wajen gudanar da babban taron ta na kasa da aka shirya yi ranar 15 ga watan Nuwamban 2025 a jihar Oyo.
Wannan na zuwa ne bayan taron gwamnonin jam’iyyar da aka yi a jihar Zamfara, inda suka fitar da sanarwa a ranar Asabar, 23 ga Agusta, suna mai kira ga mambobin jam’iyyar da su jajirce wajen tabbatar da nasarar taron.
A cikin sanarwar, wacce gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammad ya sanya wa hannu, an jaddada cewa PDP ce kadai jam’iyyar da za ta iya dawo da Najeriya kan turba, tare da jan hankalin mambobi da su yi watsi da duk wani yunkurin zagon ƙasa.
“Mun yaba da jajircewar shugabannin jam’iyyar, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar guguwar ficewa daga cikinta. Wannan tsaiko ba zai hana PDP samun karɓuwa a wajen masu zaɓe ba,” in ji sanarwar.
PDP ta kuma sake nanata burinta na ceto Najeriya daga halin da ta ce jam’iyyar APC ta jefa ta, tana mai cewa matakan gwamnati mai ci sun jefa ‘yan kasa cikin mawuyacin hali.