Rahotanni daga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC da hukumar EFCC sun gano zargin wawure naira biliyan 6.5 da ake zargin sun shafi Daraktan tsare tsare na Gwamnan Kano, Abdullahi Ibrahim Rogo.
Bisa ga takardun kotu da aka samu, ana zargin Rogo da karkatar da kudaden gwamnati ta hanyar amfani da kamfanoni kamar H&M Nigeria Limited, A.Y. Maikifi Petroleum, da Ammas Oil and Gas Limited don karɓar kuɗi kan kwangiloli na bogi.
Jaridar Daily Nigerian, ta bayyana cewa rahoton ya ce an karkatar da kudaden tsakanin watan Nuwamba 2023 zuwa Fabrairu 2025, kuma daga cikin kudaden da aka gano, an riga an karɓo sama da naira biliyan 1.1 daga hannun wasu kamfanoni.
Haka kuma, bincike ya gano cewa wani asusun banki da Rogo ke amfani da shi da sunan AH Bello Business Solutions Limited ya samu kudaden shiga na sama da naira biliyan 3 a tsakanin watan Agusta 2024 zuwa Fabrairu 2025. Kotun tarayya a Kano ta bayar da umarnin kwace ragowar naira miliyan 142.2 da ke cikin asusun tare da rufe da sauran asusun.
Duk da cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin yaki da cin hanci a gwamnatinsa, wannan bincike na iya haifar da babban kalubale ga gwamnatin Kano a fannin yaƙi da rashawa.
Rogo dai ya shigar da kara a kotun Kano yana neman dakatar da kama shi da gurfanar da shi, amma hukumomin ICPC da EFCC sun ce suna da hujjoji masu ƙarfi da ke tabbatar da laifinsa.