Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bayyana shirin gwamnatin sa na dakatar da jigilar shanu da awaki kai tsaye zuwa kasuwannin Legas da Ogun.
Ya ce maimakon haka, za a kafa cibiyar yankawa da sarrafa naman dabbobi a Mokwa, inda za a rika siyar da naman kawai zuwa yankin Kudu.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin taron ‘First Bank 2025, wanda ya mayar da hankali kan harkokin noma da kasuwanci, wanda aka gudanar a Legas.